- Yayin da Gwamnatin Tarayya ta maka gwamnoni 36 a kotu kan ƙananan hukumomi, Kotun Koli ta ba su sabon umarni
- Kotun ta bukaci duka gwamnoni 36 da su yi martani kan zarginsu da ake yi game da dakile ƴancin ƙananan hukumomi
- Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin ta shigar da korafi kan gwamnonin game da ƙananan hukumomi 774 da ke fadin ƙasar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kotun Koli ta ba gwamnonin jihohi 36 wa'adin kwanaki bakwai su yi martani kan kasarsu da aka shigar.
Kotun ta bukaci hakan ne bayan Gwamnatin Tarayya ta maka su a kotu kan ba kananan hukumomi 774 ƴancin kansu.
Kotu ta kori ƴan APC 25, ta hana su ayyana kansu a matsayin 'yan majalisa
Umarnin da kotun ta ba ministan Tinubu
Har ila yau, kotun ta umarci Ministan Shari'a ya yi martani cikin kwanaki biyu bayan karbar korafi daga gwamnonin, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai Shari'a, Garba Lawal ya ba da wannan umarni bayan korafin Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi.
Alkalin kotun ya ce sun dauki matakin ne ganin yadda korafin ke bukatar gaggawa saboda muhimmancin abin da ake kara a kai, Daily Post ta tattaro.
Ta bukaci kammala duka shari'ar cikin yan kwanaki inda kuma ta saka ranar 13 ga watan Yuni mai zuwa domin sauraran shari'ar.
Jihohin da ba su halarci zaman kotun ba
Alkalin har ila yau, ya umarci duka jihohi takwas da ba su samu halartar zaman da aka yi ba da sake ba su sabon umarni.
Jihohin da ba su samu daman halartar taron ba sun hada da Borno da Kano da Kogi da Niger da Osun da Oyo da Sokoto da kuma Ogun.
Kotu ta dakatar da Gwamna daga binciken Gwamnatin 2015 zuwa 2023 da ta shude
Gwamnatin tarayya ta maka gwamnoni a kotu
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Mai girma Bola Ahmed Tinubu ta maka gwamnonin jihohin Najeriya 36 zuwa Kotun Koli.
Matakin da aka dauka na shari’a kan gwamnoni 36 ya biyo bayan rashin da’a da ake zarginsu da aikatawa a harkokin gudanar da kananan hukumomi.
Babban lauyan Tarayya kuma Ministan shari’a, Prince Lateef Fagbemi, SAN, ya shigar da karar mai lamba: SC/CV/343/2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllboF6gZFmopqmkaOur3nHrqKupZ%2Bitm63zq2sp2WbpLmqedOaZJuZXZzEornNqKWiZWNrerStwailZq2dlr%2BvtYybmLKZnmLBqrrUm6xmsZFiuqK3wGaqrmWRYriwwNRo