Tacha: Fitacciyar Yar Najeriya Ta Saka Rigar N140m Saboda Ta Halarci Taron AMVCA

May 2024 · 3 minute read

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Tsohuwar tauraruwar shirin Big Brother Naija (BBNaija), Natacha Anita Akide, wacce aka fi sani da Tacha, ta yi wata shigar kece raini da ta ja hankalin jama'a.

Tacha ta bayyana kudin da ta kashe wajen dinka rigar da ta saka a taron ba da kyaututtuka na Africa Magic Viewers’ Choice Awards (AMVCA) karo na 10.

Kara karanta wannan

Siyasar 2027: Ka yi hankali da mutanen Arewa, Ibo sun fara gargadin Peter Obi

Kudin rigar Tacha ya kai N140m

Taron wanda ya gudana a Otal din Eko da ke Legas, a ranar Asabar kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata hira da ta yi da sanannen dan intanet, Timi Agbaje, tauraruwar ta BBNaija ta bayyana cewa rigarta ta kai darajar $100,000 (kimanin Naira miliyan 140).

“A shekarar da ta gabata kin saka rigar $20,000 a taron AMVCA. Wannan shekarar nawa kika kashe a suturarki?"

- Agbaje ya tambayi Tacha.

Tacha ta amsa da cewa: "Ta kai kusan $100,000"

Kyawawan hotunan rigar Tacha

Domin halartar taron AMVCA 2024, Tacha ta saka farar riga da aka yi mata ado da kananun duwatsun kwalliya, tare da wani kwando na ado a kafaɗarta

Jakar da ke rike a hannunta ta yi dai dai da zubin tsarin rigar, abin da ya kara fito da asalin kyawu da kuma kawar da ke tattare da wannan shiga.

Kara karanta wannan

Hukumar FIRS ta tara Naira tiriliyan 3.94 a watanni 3, ta fadi biliyoyin da take hari a 2024

Domin karawa kanta ado, Tacha ta sha kwalliya da wani leshi mai sheki da ya taso daga gadon bayanta ya sauka kasa ta yadda yake jan kasa tare da rufe duk inda ta taka.

Kalli zafafan hotunan rigar a nan kasa:

"Ba abin mamaki ba ne" - Amina Lawal

Ko da muka tuntubi Amina Lawal, wata mai dinka sutura a jihar Kaduna, ta ce ba abin mamaki ba ne don jaruma Tacha ko jarumai sun saka sutura mai tsada.

Ta ce sau tari ana ganin mawaka, 'yan fim, ko wasu fitattu suna saka suturun sama da Naira miliyan 100 idan za a yi taro, to amma ba su ke siya da kudinsu ba.

Amina ta ce mafi akasari, sukan nemi kwararrun kamfanoni ko masu dinka suturu domin yin hadin guiwa.

"Za su saka kayan ne domin tallata kamfanin ko mai dinkin. Ba lallai su biya kudin ba, amma babbar alaka ce.

Kara karanta wannan

"An yi amfani da bam": Mutum 1 ya mutu da aka bankawa masallata wuta a Kano

"A nan Arewa, na kan dinka kaya ga jarumai in ba su kyauta, buri na shi ne idan sun saka hoto a soshiyal midiya su rubuta cewa ni ce na dinka kayan."

Charterhouse Lagos: Firamare da ake biyan N42m

A wani labarin, mun ruwaito maku cewa an bude wata makarantar firamare mai Charterhouse a Lagos wada ake biyan Naira miliyan 42 a shekara.

Duk da cewa ginin makarantar abin kwatance ne, sai dai 'yan Najeriya da dama sun yi adawa da makudan kudaden da makarantar ta saka ga yaran firamare.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC51K2Yp51fZoJ6fo9saWaskZi1onnFoquam5OexqK%2BjLKYq2WelremvsiymGaskWKxqrrKmmSroZeWv266kG1npmWjlq%2BwsMBmq5plmJa5or7ComStmaKku26tzK%2Bammc%3D