Gudaji Kazaure: Kudin da Aka Sace Ya Fi Karfin N70tr ko N80tr, Na Nuna Inda Aka Boye Su

June 2024 · 3 minute read

Abuja - Dan majalisar wakilai, Muhammad Gudaji Kazaure ya yi magana da manema labarai bayan mataimakiyar Gwamnan CBN ta bayyana a gaban ‘yan majalisar tarayya.

Legit.ng Hausa ta ci karo da bidiyon nan na Hon. Muhammad Gudaji Kazaure a Twitter, inda aka ji yana zargin shugabannin majalisa da hana shi magana.

‘Dan majalisar ya ce mataimakin shugaban majalisar wakilar tarayya ya bada shawarar ka da a bar shi ya ce komai da ake yi wa Aisha Ahmed tambayoyi.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Dawo da Komai Baya, Ya Fadi Gaskiyar Batun Haduwarsa da Gwamnonin PDP

Gudaji Kazaure yana ganin cewa duk tambayoyin da aka yi wa Aisha Ahmed wanda ta wakilci Godwin Emefiele, ba a tabo halin da tattalin arzikin kasa ke ciki ba.

Abin da ya faru a ranar - Gudaji Kazaure

"Idan ku ka duba lamarin, lokacin da na shiga zauren majalisa a yau (ranar), domin mataimakiyar Gwamnar CBN ta na nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Na zo a makare, amma na gaggauta na gana da ita. Da na daga hannu na, shugaban majalisa ya yi niyyar kyale ni in yi magana.Amma sai mataimakin shugaban majalisa ya ba shi shawara ka da a bar ni in yi magana. Shakka babu, dole ‘Yan Najeriya su san dalilin mataimakin shugaban majalisa nah ana a bar ni in yi wa Gwamnar CBN tambayoyi.Na zo da duka takardu na, domin a duk abubuwan da suka tambaye ta, ba su yi maganar halin da tattalin arzikin kasa yake ciki ba.

Kara karanta wannan

Kungiyar ASUU ta Bayyana Wanda Ya Yaudare su Aka Janye Yajin-Aiki a Jami’o’i

- Hon. Muhammad Gudaji Kazaure

Kudin sun isa a biya bashin Najeriya

Gudaji Kazaure ya dage a kan cewa babban bankin kasa ya boye wasu makudan kudi da za su isa a biya duk wani bashi da ake bin gwamnatin Najeriya.

“Na tabbata ‘yan jarida kun samu labari mun fitar da wasu takardu ta hannun Point Blank News. Mun fitar da akawunt na banki 29 inda N70tr suke, su na nan. Kudin nan sun zarce N70tr ko N80tr da muke ambata. Amma meyasa aka hana ni magana? Tambayar farko da ya kamata ayi kenan.

- Hon. Muhammad Gudaji Kazaure

Ta ya za ayi ciniki babu bankuna a kauyuka?

A cewar Hon. Gudaji Kazaure, tambayar farko da za a jefa kenan, sannan tambaya ta biyu ita ce yadda za ayi mu’amala ba tare da takardun kudi ba a kauyuka.

‘Dan siyasar ya ce a kauyuka babu bankuna don haka babu wata hanyar ciniki idan aka takaita kudin da ke yawo, ya ce dole ne gwamnati ta canza tsarin ta.

Kara karanta wannan

Da Dumi-ɗumi: Hadimin Gwamnan Jam'iyyar APC Ya Mutu a Hatsarin Mota

Kazaure ya ce akwai bukatar gwamnati ta san cewa ‘yan kauye ba su da banki ko karfin sabis da za su iya amfani da katin ATM ko na’urar POS wajen cire kudi.

Gudaji Kazaure ya yi wa Garba Shehu raddi

Kwanaki an samu rahoto, Hon. Gudaji Kazaure ya maidawa Fadar Shugaban kasa da Garba Shehu martani a kan binciko satar Naira Tiriliyan 80 da aka yi a CBN.

‘Dan majalisar yace tsohon ‘dan sandan nan, Muhammad Wakili da aka fi sani da Singham, yana cikin ‘yan kwamitin da suka yi aikin bankado satar da aka yi.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC%2FyLKYrJlfZoJyfZNtb2aZkp67brDAZpikmV2orqSxjLKYZp6ZYriivsWipWamZ2XBs3nKqGSncGCpv2651KdkraeelnqqusOaZJqjkWKvsMXEZqKunJmjeqyt2Zqsq51f